Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika wa majalisar dattawa da buƙatar tantancewa da tabbatar da sabbin hafsoshin tsaro da ya nada kwanan nan.
An karanta wasikar shugaban ƙasar a zauren majalisar ranar Talata ta hannun shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Sabbin shugabannin da aka mika sunayensu sun haɗa da:
Janar Olufemi Oluyede – Babban Hafsan Tsaro (CDS)
Manjo Janar Waheedi Shaibu – Hafsan Sojan Kasa (COAS)
Rear Admiral Idi Abbas – Hafsan Sojan Ruwa (CNS)
Air Vice Marshal Kennedy Aneke – Hafsan Sojan Sama (CAS)
Manjo Janar Emmanuel Undiendeye – Hafsan Leken Asiri na Tsaro (CDI)
Bayan karanta wasikar, Akpabio ya umurci cewa a mika sunayen waɗanda aka zaɓa ga Ɗaukacin Kwamitin Majalisar domin gudanar da tantancewa da tabbatarwa a mako mai zuwa.


