Babban Sufeton ‘Yan sandan ƙasa Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda za ta tura jami’ai 45,000 domin tabbatar da tsaro a yayin zaben gwamnan jihar Anambra da za a gudanar a ranar 8 ga Nuwamba, 2025.
Egbetokun, wanda ke jagorantar rundunar kai ɗaukin gaggawa ta ‘yan sanda, ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin taron kwamitin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) da aka gudanar a Abuja.
Ya ce jami’an da za a tura za su tabbatar da tsaro kafin, a lokacin, da kuma bayan kammala zaben.
Babban Sufeton ya ƙara da cewa an shirya fara tura jami’an daga ranar 1 ga Nuwamba domin dakile duk wata barazana da ka iya shafar gudanar da zaben.
Haka kuma, Egbetokun ya bayyana cewa, baya ga jami’an ‘yan sanda, sauran hukumomin tsaro kamar DSS, Civil Defence, sojoji da hukumar farin kaya za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyi a lokacin zaben.


