Najeriya ta fara fitar da Fanal ɗin Sola zuwa ƙasashen waje —Gwamnatin tarayya 

0
14

Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Najeriya ta kaddamar da fitar da na’urorin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da ake kera wa a cikin gida zuwa ƙasar Ghana, wani babban ci gaba da yake nuna ƙarfafa masana’antar makamashin a ƙasar.

Adelabu ya sanar da haka ne yayin taron ƙarawa juna sani akan harkokin lantarkin Najeriya na shekarar 2025, da aka gudanar a Legas, inda ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na faɗaɗa amfani da makamashi mai dorewa ta hanyar haɗin gwiwa da kamfanonin masu zaman kansu da kuma bunƙasa masana’antu.

Ya ce duk da ƙarancin kuɗin gwamnati, shiga cikin harkar masana’antu daga ɓangaren masu zaman kansu ne zai taimaka wajen aiwatar da manyan ayyuka, cike gibin ababen more rayuwa da kuma buɗe damar samar da makamashi mai inganci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here