Al’ummar yankin Garoua da ke arewacin ƙasar Kamaru na ci gaba da gudanar da zanga-zanga don nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka kammala kwanan nan.
Hukumar zaɓe ta ƙasar ta bayyana shugaba Paul Biya, wanda yanzu yana da kimanin shekaru 92, a matsayin wanda ya sake lashe zaɓen, abin da ke nufin zai ci gaba da rike mulki bayan kusan shekara 42 yana jagorantar ƙasar.
Sai dai wannan sanarwa ta tayar da ƙura a wasu sassan ƙasar, musamman a yankin Garoua, inda jama’a ke zargin cewa an tafka maguɗi a lokacin zaɓen. Masu zanga-zangar suna kira da a binciki yadda aka gudanar da zaɓen, tare da neman tabbatar da adalci da gaskiya.
Abokin hamayyarsa, Issa Bakary, ya bayyana cewa shi ne ya lashe zaɓen bisa sahihan kuri’u, yana mai zargin cewa an shirya sakamakon ne don Paul Biya, ya ci gaba da riƙe mulki.
‘Yan sanda da jami’an tsaro sun baza jami’ai a yankin domin dakile rikice-rikice, yayin da gwamnati ke kira ga jama’a da su zauna lafiya tare da barin hukumomi su bi diddigin korafe-korafen da aka gabatar.


