Sule Lamido Ya Yi Barazanar Shigar Da Jam’iyyar PDP Ƙara a Kotu

0
11

Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya yi barazanar kai jam’iyyar PDP kotu idan ta hana shi samun fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar.

Lamido ya ce ya je ofishin PDP na ƙasa a Abuja domin sayen fom ɗin, amma ofishin da ke sayar da fom ɗin a rufe yake, kuma jami’an jam’iyyar sun ce ba su san inda fom ɗin yake ba.

Daga baya aka shaida masa cewa fom ɗin yana hannun gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda ke jagorantar shirya babban taron jam’iyyar.

Lamido ya ce bai dace PDP ta ɓoye bayanai ko ta nuna son kai ga wasu ba, yana mai cewa idan bai samu fom ba, zai kai ƙara kotu.

Ya kuma gargadi jam’iyyar da ta kiyaye tsarin dimokuraɗiyya idan tana son samun nasara a zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here