Kuɗin hayar ɗaki a Abuja ya zarce albashin wasu maaikata na shekaru 3

0
8

Farashin haya a babban birnin tarayya Abuja ya ƙaru fiye da kima, abin da ya tilasta wa mazauna da dama barin birnin zuwa wuraren da haya ta fi sauƙi kamar Mararaba, Masaka, Suleja da Madalla.

Rahoton Daily Trust ya gano cewa yawancin masu gida yanzu suna karɓar kuɗin haya na shekara biyu a lokaci ɗaya, yayin da haya a wuraren Maitama, Asokoro da Guzape ke kaiwa sama da Naira 3 miliyan ga ɗaki ɗaya.

Mazauna da dama sun koka cewa albashinsu ba ya ƙaruwa yayin da hayar gidaje ke ƙaruwa fiye da kima. Wasu sun ce gwamnati ba ta samar da gidaje masu arha ga ma’aikata ba, kuma harkar haya bata da tsari ko kulawa daga hukumomi.

Masu gidaje sun ce hauhawar farashin kayan gini, haraji da tsadar gyara ne ke tilasta musu ƙara kuɗin haya. Masana harkar gidaje kuma sun danganta matsalar da ƙarancin gidaje.

A wannan yanayi ma’aikaci mai karɓar mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70, sai yayi aikin fiye da shekaru 3 kafin ya samu Naira miliyan 3, da ake biyan da hayar ɗaki ɗaya a wasu sassan Abuja.

A shekara uku ƙaramin ma’aikaci mai karɓar mafi ƙarancin albashi zai karɓi Naira miliyan 2,520,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here