Akalla makiyaya goma ne suka mutu a wani harin ramuwar gayya da aka kai wa wani sansanin Fulani a ƙauyen Tilli, dake karamar hukumar Bunza, Jihar Kebbi.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Daily Trust cewa harin ya biyo bayan kisan wani ɗan sa kai da aka alakanta da wasu Fulani da ke zaune a yankin.
“An kai harin bisa kuskure. Sun ɗauka Fulani ne suka kashe ɗan sa kai,” in ji wani mazaunin yankin. “An kashe mutane sama da goma, kuma har yanzu ana binciken ko akwai ƙarin waɗanda suka mutu.”
Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah, tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Tafida, sun ziyarci yankin domin jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce bai samu rahoton lamarin ba tukuna, amma ya yi alkawarin bincike.


