Tsoffin manyan hafsoshin tsaron da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke daga mukamansu Janar Christopher Musa (tsohon Hafsan Tsaron Ƙasa), Air Marshal Hasan Abubakar (tsohon Hafsan Sojan Sama), da Vice Admiral Emmanuel Ogalla (tsohon Hafsan Sojan Ruwa) za su karɓi kyautar sabbin motocin da harsashi ba ya iya ɓulawa.
Bugu da ƙari, za a samar musu da ma’aikata na musamman da za su riƙa yi musu hidima a gida tare da kula da lafiyarsu kyauta har zuwa ƙarshen rayuwarsu.
Wannan fa’idar na daga cikin sabbin ƙa’idojin barin aikin soji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da su a ranar 14 ga Disamba, 2024.


