Majalisun dokokin ƙasa sun amince a kirkiro sabbin jihohi masu

0
83

Majalisun Dokokin Tarayya sun amince da shirin ƙirƙirar jihohi shida sabbi, abin da zai ƙara yawan jihohin ƙasar nan daga 36 zuwa 42 idan aka amince da hakan.

Wannan shawara ta fito ne daga wani taron kwanaki biyu na Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Dattawa da ta Wakilai kan Sauye-sauyen Tsarin Mulki da aka gudanar a Legas, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu.

Sanarwar da aka fitar bayan taron ta bayyana cewa, kwamitin ya tattauna kan dokoki 69 da ke neman gyaran tsarin mulki, ciki har da buƙatun ƙirƙirar jihohi 55, gyaran iyaka guda biyu, da kuma buƙatun ƙirƙirar kananan hukumomi 278.

Bayan dogon nazari, ‘yan majalisar sun cimma matsaya ɗaya cewa a ƙirƙiri sabuwar jiha ɗaya a kowace shiyya, Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Yamma, Kudu maso Kudu, da Kudu maso Gabas.

Rahoton wannan shawara zai shiga cikin rahoton kwamitin da ake sa ran gabatarwa a majalisun biyu a farkon watan Nuwamba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here