Rundunar Hisba ta jihar Kano ta kama mutum 25 bisa zargin shirya bikin auren masu neman maza a yankin Hotoro da ke cikin birnin Kano.
Mataimakin kwamandan hukumar, Mujahedeen Aminudeen, ya bayyana cewa jami’an Hisba sun kai samame a cibiyar taro ta Fatima Event Centre a ranar Asabar, 25 ga Oktoba 2025, inda suka kama mutum 18 maza da mata bakwai.
A cewar Aminudeen, wadanda aka kama sun haÉ—a da wanda ake zargi da yin aure da kuma baki daga wurare daban-daban kamar Sheka, Yar Gaya da Kofar Nasarawa.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da yaki da duk wani abin da take ɗauka a matsayin ayyukan rashin tarbiyya, tare da jan hankalin jama’a da cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai bata sunan Kano ba.


