Ƴan kasuwa sun yi kukan karyewar farashin shinkafa

0
9

Farashin shinkafa ya fadi a kasuwannin Legas sakamakon karuwar shigo da kaya daga ketare da kuma girbin cikin gida da ya karu, wanda hakan ya sa masu saye suka samu sauƙi amma ’yan kasuwa suna yin kukan shiga asara.

Rahotanni sun nuna cewa buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 yanzu yana tsakanin ₦55,000 zuwa ₦70,000, yayin da a farkon shekara ake sayar da shi har ₦95,000.

A kasuwannin Oyingbo, Arena, Festac Town da Mile 12, shinkafar gida da ake sayarwa ₦85,000 a watan Janairu yanzu ta koma ₦60,000 zuwa ₦70,000, yayin da ta waje ke tsakanin ₦65,000 da ₦75,000.

“Ina sayarwa da asara,” in ji Precious Okoro, ɗaya daga cikin ’yan kasuwa a Arena. “Na saya buhu ₦85,000, yanzu ina sayar da ₦65,000. Saukar farashin ta zo ba zato.”

Wasu ’yan kasuwa sun bayyana cewa farashin ya fara sauka tun watan Agusta bayan bude iyakoki da kuma karuwar kaya daga Arewa da ƙasashen makwabta.

“Masu saye suna farin ciki, amma mu ’yan kasuwa muna kuka,” in ji Odion Michael, ɗan kasuwa a Mile 12. “Muna so farashi ya daidaita, ba ya hauhawa ko faɗuwa kwatsam ba.”

Masana harkar noma sun yi gargadin cewa wannan saukar farashin ba za ta daɗe ba, domin rashin daidaiton kasuwa na iya jawo tashi kafin ƙarshen shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here