Rundunar ‘yan sanda ta jihar Sokoto ta kama wasu masoya biyu da ake zargi da haɗa baki wajen kashe wani matashi mai suna Ali Salisu a ƙauyen Gidan Kacha, ƙaramar hukumar Gada ta jihar.
A cewar sanarwar da kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufai, ya fitar a ranar Asabar, lamarin ya faru ne a ranar 4 ga Oktoba, 2025, lokacin da budurwar mamacin, Rukayya Amadu, ta gayyace shi zuwa daji a Dabagi don ganawa da shi.
Sai dai bisa ga rahoton ‘yan sanda, Rukayya ta shirya makirci tare da wani saurayinta na biyu, Hamisu Ibrahim, inda suka kulla maƙarƙashiya don sace masa babur da kuma kashe shi.
Da Ali ya isa wurin, Hamisu ya taso masa a guje, ya ɗaure masa wuya da igiya har lahira sannan ya gudu da babur ɗinsa kirar Kasea.
Binciken da aka gudanar daga baya ya kai ga kama wasu mutane biyu Lawali Abdullahi da Ibrahim Abdullahi — waɗanda ake zargi da karɓar babur ɗin da aka sace ba tare da bincike ba.
DSP Rufai ya tabbatar da cewa an kama dukkanin waɗanda ake zargi huɗu kuma ana tsare da su, sannan za a gurfanar da su gaban kotu bisa laifukan haɗin baki, kisan kai, fashi da karɓar kayan sata.


