Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin rushe shugabancin Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye ta jihar.
A cewar sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ya fitar a ranar Asabar, 25 ga Oktoba 2025, matakin ya biyo bayan dogon rikicin shugabanci da ke addabar hukumar duk da ƙoƙarin sulhu da gwamnati ta yi.
Sanarwar ta bayyana cewa an sallami shugaban hukumar, sakatare, da sauran mambobi gaba ɗaya, tare da umartar su da su mika dukkan kayayyakin gwamnati da takardun gwamnati da ke hannunsu ga babban jami’in hukumar kafin ranar Litinin, 27 ga Oktoba 2025.
Haka kuma, an bukace su da su mika cikakken rahoton mika aiki ga Ofishin Sakataren Gwamnati da na Kwamishinan Ma’aikatar Kasuwanci.


