Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU) ta musanta wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke zarginta da hannu a cikin aikin ƙirƙirar makaman nukiliya a Najeriya.
Daraktan yada labarai na jami’ar, Auwalu Umar, ya bayyana a wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar cewa bidiyon da aka ƙirƙira ta hanyar AI ba gaskiya ba ne, kuma manufarsa ita ce yaudarar jama’a game da shirin makamashin nukiliya a Najeriya.
Ya ce zargin cewa masana na ABU sun taɓa samun kayan aikin ƙirƙirar makami daga cibiyar AQ Khan ta Pakistan ko yin gwajin uranium a Kaduna a shekarun 1980 ba gaskiya bane .
Umar ya ƙara da cewa a lokacin da ake zargin, yawancin masana a cibiyar binciken makamashin nukiliya ta jami’ar (CERT) suna ci gaba da karatu a ƙasashen waje, kuma babu wata shaida da ke nuna an taɓa yin aikin da ya saba wa doka.


