Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa wajen gyara tsarin tsaron sararin samaniyar ƙasa, domin hana amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-haren kungiyar Boko Haram.
Zulum ya bayyana hakan ne a garin Mafa ranar Juma’a, bayan wani hari da ‘yan Boko Haram suka kai, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
“Ina da labarin cewa maƙiya sun fara amfani da jirage marasa matuƙa a hare-harensu, musamman a Dikwa. Wannan lamari ne mai matuƙar tayar da hankali,” in ji shi.
Gwamnan ya ce yawaitar irin waɗannan jirage a hannun ƴan ta’adda na iya haifar da barazana ga tsaron ƙasa, don haka ya kamata a ɗauki matakan gaggawa wajen daƙile wannan sabon salo.
Zulum ya kuma jaddada buƙatar ƙarfafa tsaro a bakin iyakokin ƙasa da kuma inganta hanyoyin lura da sararin samaniya, yana mai cewa: “Wannan abu ne da ya kamata a aiwatar nan take ba tare da ɓata lokaci ba.”


