Fiye da manyan hafsoshin soja 160 za su yi ritayar dole 

0
9

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke manyan hafsoshin tsaron ƙasa tare da na rundunonin soja, ruwa da sama, sannan ya naɗa sabbi.

An naɗa Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon hafsan hafsoshin ƙasa  (CDS), yayin da Manjo Janar W. Shaibu ya karɓi kujerar Shugaban Rundunar Soja (COAS). Haka kuma, Air Vice Marshal S.K. Aneke ya zama sabon Shugaban Rundunar Sama (CAS), sai Rear Admiral I. Abbas da aka naɗa Shugaban Rundunar Ruwa (CNS).

Sai dai wannan sauyi ya janyo wani babban sauyin cikin rundunar tsaro, inda sama da manyan hafsoshin soja 160 za su tafi ritaya saboda tsarin matsayin soja da yake buƙatar manyan da suka fi sabbin shugabanni girma su ajiye aiki.

A cewar rahoto, sojoji fiye da 120 daga rundunar ƙasa ne abin zai shafa, yayin da na rundunar sama da ruwa ke kusan 40. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here