Wasu ƴan bindiga sun kai hari kan wata motar fasinja a tsakanin garuruwan Eruku da Egbe, da ke iyakar jihohin Kwara da Kogi, inda suka bude wa motar wuta.
Shaidu sun bayyana cewa harin ya faru ne da rana a ranar Asabar lokacin da maharan da suka fito daga daji suka bude wuta kan motar da ke kan hanyar Ilorin–Egbe.
Rahotanni sun nuna cewa direban motar, wanda ɗan asalin Isanlu ne, ya ji rauni sakamakon harbin bindiga.
Wani bidiyo da aka gani ya nuna motar cike da ramukan harsasai da kuma jinin da ya zubo a gefen direba.
Mutanen yankin sun roƙi shugabannin ƙananan hukumomin Yagba East da Yagba West su haɗa kai wajen dakile yawaitar hare-haren da ke faruwa a hanyar.
Hanyar Ilorin–Egbe, wacce ke da muhimmanci ga matafiya da ƴan kasuwa, ta zama sananniya wajen faruwar irin waɗannan hare-hare a ‘yan watannin nan, abin da ya haddasa tsoro ga masu zirga-zirga.


