Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke manyan hafsoshin tsaro na ƙasa, ciki har da Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, tare da naɗa sabbin shugabanni a rundunonin soji.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya fitar a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, an naɗa Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon Babban Hafsan Tsaro, wanda kafin wannan lokaci ya kasance Babban Hafsan Sojan Ƙasa.
Haka kuma, Manjo-Janar W. Shaibu shi ne sabon Babban Hafsan Sojan Ƙasa, yayin da Air Vice Marshal S.K. Aneke ya zama Babban Hafsan Sojan Sama, sannan Rear Admiral I. Abbas aka naɗa a matsayin Babban Hafsan Rundunar Ruwa.
Sai dai Manjo-Janar E.A.P. Undiendeye, wanda ke rike da mukamin Babban Daraktan Leken Asiri na Tsaro (Defence Intelligence), ya ci gaba da rike matsayinsa.


