Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, da ya tabbatar da gaskiya da adalci a shirye-shiryen gudanar da zaɓen 2027, tare da guje wa duk wani nau’in tashin hankali.
Tinubu ya yi wannan jawabi ne a fadar shugaban ƙasa dake Abuja, jim kaɗan bayan ya rantsar da Farfesa Amupitan, wanda majalisar dattawa ta tabbatar da nadin sa mako guda da ya gabata.
Shugaban ƙasar ya ce wannan nadi alama ce ta amincewa da ƙwarewa da gaskiyar Farfesan daga ɓangarorin zartarwa da na majalisa.
Ya ƙara da cewa: “Ina roƙonka Farfesa Amupitan, ka kare mutuncin zaɓe da tsarin gudanarwa, da kuma ƙarfin gwiwar hukumar INEC. Ina yi maka fatan alheri a aikin ka na farko a watan Nuwamba 2025, wanda shi ne zaben gwamnan Jihar Anambra.”
Tinubu ya bayyana cewa shugabancin Amupitan zai kasance kalubale mai girma amma mai albarka, yana mai jaddada cewa ya kamata ya yi aiki da gaskiya, jajircewa, da kishin ƙasa domin tabbatar da zaman lafiya da amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyya.


