Sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya sha alwashin kare dokokin zaɓe da kuma bin ƙa’idojin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Yayin da yake magana bayan rantsar da shi a Abuja ranar Alhamis, Farfesa Amupitan ya bayyana cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarce shi da tabbatar da gudanar da zaɓe mai inganci da gaskiya a fadin ƙasar.
Ya ce, “Ba kawai zan tabbatar da ingancin zaɓe ba, har ma zan haɗa kai da duk masu ruwa da tsaki domin nasara ba ta samu sai da haɗin gwiwa.”
Amupitan shi ne shugaban hukumar zaɓen Najeriya na shida tun bayan komawar ƙasar kan tafarkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.


