Farashin kayan abinci ya yi raga-raga a wasu kasuwannin Abuja, manoma sun koka

0
7

Rahotanni daga sassa daban-daban na Babban Birnin Tarayya (FCT) sun nuna cewa farashin kayan abinci ya sake yin ƙasa sosai sakamakon girbin bana da manoma suka samu.

A kasuwannin Abaji, Kwaita, Dobi, da Kwaku, an gano cewa farashin shinkafa, wake, gero, dawa, da masara ya ragu da kusan kashi 50 zuwa 65 cikin ɗari.

A kasuwar Abaji, mudu ɗaya na shinkafa wanda ake sayarwa da Naira 2,000 a baya yanzu ya koma tsakanin Naira 1,300 da Nnaira 1,500. Haka nan mudu na wake daga Naira 2,500 ya koma Naira 2,000, yayin da masara ta sauka daga Naira 800 zuwa Naira 350.

Wani ɗan kasuwa a Kwaita, Malam Garba Abdullahi, ya bayyana cewa “gagarumin girbi da manoma suka samu” shi ne babban dalilin da ya sa farashi ya faɗi, sai dai ya ƙara da cewa rashin kuɗi a hannun jama’a yana hana siyan kayan sosai.

Haka kuma, a kasuwar Dobi da Kwaku, rahotanni sun tabbatar da cewa buhun masara daga Naira 30,000 ya koma Naira 18,000, yayin da buhun dawa ya sauka daga Naira 35,000 zuwa Naira 25,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here