Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa shi ne ya ƙi amincewa da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a matsayin wanda zai gaje shi bayan ya sauka daga mulki a 2007.
Obasanjo ya bayyana haka ne a Abeokuta, inda ya ce tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Osita Chidoka, ne ya kawo masa shawarar tsayar da El-Rufai, takarar shugabancin Najeriya a wancan lokaci
“Chidoka yana matsa cewa abokinsa El-Rufai ya dace da shugabanci, amma na ce yana buƙatar ya ƙara ƙwarya a fannoni daban daban,” in ji Obasanjo.
Ya ƙara da cewa daga baya Chidoka ya amince cewa ya yi daidai da naƙi amincewa da shawarar bawa El-Rufa’i takara.
Obasanjo ya yabawa El-Rufai da sauran matasan da suka yi aiki a gwamnatinsa saboda ƙwazo da basira, yana mai cewa shugabanci nagari yana buƙatar hali, kwarewa, da horo.


