An nemi mu ƙirƙiro sabbin jihohi 55 a Najeriya–Barau

0
20

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya bayyana cewa kwamitin haɗin gwiwa na majalisun dokoki kan sake nazarin kundin tsarin mulki na 1999 yana duba buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da ƙananan hukumomi 278, tare da gyaran iyaka guda biyu.

A cewar Barau, an shafe shekaru biyu ana tattaunawa da jama’a da kungiyoyi domin tattara ra’ayoyi kan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar nan. Ya ce burin majalisar shi ne a mika gyaran farko ga majalisun jihohi kafin ƙarshen shekara.

Ya jaddada cewa duk da bambance-bambancen siyasa da kabila, ‘yan majalisa su mayar da hankali kan abin da zai amfanar da Najeriya, ba tattaunawa mai rarrabuwa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here