Al’ummar Shanono sun koka a kan yadda yan bindiga ke shigo musu daga wata jihar Arewa

0
6

Al’ummar karamar hukumar Shanono da ke Jihar Kano sun koka kan yadda ’yan bindiga daga Jihar Katsina ke kai musu hare-hare tun daga shekarar 2022 har yanzu.

Shugaban kwamitin tsaron Faruruwa, Yahaya Umar Bagobiri, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan na shigowa ne da babura sama da 50, suna kashe mutane, yin garkuwa da su, da kuma satar dabbobi.

A cewarsa, “Mun fuskanci matsalar tsaro mai tsanani tsawon shekaru uku. ‘Yan bindiga daga Katsina ke shigowa Faruruwa da kewaye, suna kashe mutane, suna yin garkuwa da su, suna kuma satar dabbobi.”

Bagobiri ya ce shanu fiye da 1,600 aka sace daga shekarar 2022 zuwa yanzu, baya ga awaki, raguna da babura da dama da suka salwanta. Ya kara da cewa wasu ƙauyuka a yankin sun zama kufai saboda jama’a sun tsere zuwa Katsina domin tsira da rayukansu.

Ya roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf su turo jami’an tsaro domin kawo ƙarshen wannan ta’addanci. Ya ce akwai buƙatar gwamnati ta haɗa kai da sojoji da ’yan sanda don dawo da zaman lafiya a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here