Abubuwan da ya kamata ku sani akan sabbin hafsoshin tsaron ƙasa

0
14

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauya manyan hafsoshin tsaron ƙasa, tare da nada sabbin shugabanni huɗu don jagorantar rundunonin soja, bayan jita-jitar yunƙurin juyin mulki.

Sanarwar ta fito ne daga mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Sunday Dare, wanda ya bayyana cewa wannan mataki na cikin sabon tsarin da gwamnati ke yi don ƙarfafa tsaron ƙasa da inganta jagorancin sojoji.

Ga cikakken bayani kan sabbin hafsoshin tsaron:

1. Janar Olufemi Oluyede – Babban Hafsan Tsaro (CDS)

Shugaba Tinubu ya nada Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin sabon Babban Hafsan Tsaro, wanda ya maye gurbin Janar Christopher Musa.

Kafin nadin nasa, Oluyede ya kasance mukaddashin Hafsan Rundunar Sojoji bayan rasuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Ya kuma rike mukamin kwamandan rundunar Infantry Corps ta Jaji, Kaduna, kuma ɗan ajin 39 na makarantar horar da sojoji ta NDA.

2. Manjo Janar Shuaibu Waidi – Hafsan Sojin Ƙasa (COAS)

Waidi ya karɓi ragamar rundunar sojin ƙasa daga Manjo Janar Gold Chibuisi.

Kafin haka, ya kasance kwamandan aikin Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas, inda ya jagoranci yaƙi da Boko Haram da ISWAP.

A lokacin mulkinsa a 7 Division Maiduguri, an samu nasarori masu yawa har da mika wuya daga hannun ‘yan ta’adda.

3. Air Vice Marshal Sunday Kelvin Aneke – Hafsan Sojin Sama (CAS)

Aneke wanda aka haifa a ranar 20 ga Fabrairu 1972 a Makurdi, ya fito daga ƙaramar hukumar Udi ta jihar Enugu.

Ya fara karatunsa a Army Children School da Government College Kaduna, sannan ya shiga NDA a 1988.

Ya na da digiri a Physics, ya kuma yi karatu a wasu jami’o’in Amurka da Najeriya.

4. Rear Admiral I. Abbas – Hafsan Rundunar Sojin Ruwa (CNS)

Rear Admiral Abbas shi ne sabon hafsan rundunar sojin ruwa. Ya kasance ɗan asalin jihar Kano.

5. Meja Janar E.A.P. Undiendeye – Ya Ci Gaba da Riƙe Matsayinsa a Hukumar Leken Asiri (CDI)

Shi ne kadai cikin manyan hafsoshin da aka bar masa mukaminsa. Wannan na nuna cewa gwamnati na son ci gaba da amfani da kwarewarsa a fannin leken asiri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here