Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan (SAN) a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
An gudanar da taron rantsuwar ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, tare da halartar manyan jami’an gwamnati da shugabannin majalisar dokoki.
Farfesa Amupitan, ɗan asalin ƙaramar hukumar Ijumu a Jihar Kogi, ya gaji Farfesa Mahmood Yakubu, wanda wa’adinsa ya ƙare.
An amince da nadinsa ne bayan majalisar koli ta amince da sunansa kuma majalisar dattawa ta tabbatar da shi.