Jagoran ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biapra IPOB, Nnamdi Kanu, ya kori dukkan lauyoyinsa tare da bayyana cewa zai kare kansa da kansa a kotu.
A zaman shari’ar da aka ci gaba da saurara a yau Alhamis, Kanu ya sanar da kotu cewa ba ya buƙatar wakilcin lauyoyi, kuma a shirye yake ya kare kansa.
Bayan wannan sanarwa, babban lauya a tawagar lauyoyin, Kanu Agabi (SAN), ya bayyana cewa shi da sauran lauyoyin da suka haɗa da Onyechi Ikpeazu, Paul Erokoro, Joseph Akubo da Emeka Etiaba sun janye daga shari’ar domin girmama shawarar Kanu.
Alkalin kotun, Mai Shari’a James Omotosho, ya tambayi Kanu ko gaskiya ne zai kare kansa, kuma ya tabbatar da hakan. Daga nan sai alkalin ya umarci sauran lauyoyin da su bar kotu.
Kanu ya fara kare kansa da magana kan hurumin kotun a shari’ar, amma alkalin ya ƙi amincewa da hujjar tasa, yana mai cewa ya ci gaba da kare kansa.
Sai dai ɗaya daga cikin lauyoyin da suka janye, Ikpeazu, ya roƙi kotu ta bawa Kanu lokaci domin ya shirya. Lauyan gwamnati bai yi adawa da hakan ba, wanda hakan ya sa alkalin ya dage zaman zuwa gobe, Juma’a 24 ga Oktoba, domin ci gaba da shari’ar.