Kotun Kano ta umarci wasu ƴan TikTok su riƙa wanke banɗakin Hisbah da hukumar tace fina-finai

0
10

Kotun majistire mai lamba 7 da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Halima Wali, ta yanke wa fitattun masu amfani da TikTok, Abba Sa’ad, wanda aka fi sani da Abba Minister, da Faruk Abubakar Tudun Murtala, hukuncin aikin wankewa da share harabar hukumomin gwamnati na tsawon kwanaki goma (10) saboda yada bidiyon batsa.

Kotun ta umurci Abba Minister da ya wanke bandakuna da share harabar Hisbah ta Jihar Kano na tsawon kwanaki goma, ba tare da damar biyan tara ba. Haka kuma, Faruk Abubakar ya samu irin wannan hukunci na yin aikin wankewa da share harabar Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano.

’Yan sanda ne suka gurfanar da su a gaban kotu bayan korafin da Hukumar Tace Fina-finai ƙarƙashin jagorancin Abba Almustapha ta shigar, bisa zargin su da yin bidiyo da rawar sabawa tarbiyya da ƙa’idojin addinin Musulunci.

Mai gabatar da ƙara, Barista Garzali Maigari Bichi, ya karanta musu tuhumar, inda suka amsa laifinsu nan take.

Bayan sauraron shari’ar, kotu ta yanke musu hukuncin aikin wankewa da sharewa na kwanaki goma, tare da umarnin su nemi afuwar jama’ar Kano ta kafafen sada zumunta da suke amfani da su, sannan su yi alƙawarin cewa ba za su sake aikata irin wannan laifi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here