Kotu ta fara hukunta masu zube kayan gini akan titunan Kano

0
23

Wata kotun Tafi da Gidan a jihar Kano ta rufe wani gidan wanka da ke kan titin France Road, tare da bai wa wani gidan abinci wa’adin awa 24 domin gyara bandakin sa da kuma tsaftace wajen cin abinci.

Kotun ta dauki wannan mataki ne bayan hukumar Kwashe Shara da Tsaftar Muhalli ta Jihar Kano (REMASAB), ƙarƙashin jagorancin Dr. Muhammad S. Khalil, ta gano cewa wuraren ba su bi ka’idar tsafta ba, duk da gargadin da aka riga aka yi musu.

Bugu da ƙari, kotun ta hukunta wasu mutane da aka kama da laifin zuba duwatsu, yashi da sauran kayan gini a kan titin Sabon Gari, wanda hakan ya toshe magudanar ruwa a yankin.

Lauyar gwamnati, Bahijja H. Aliyu, ce ta gabatar da ƙarar a gaban kotu, inda wadanda ake tuhuma suka amsa laifinsu.

Mai shari’a Halima Wali ta yanke musu hukuncin tara naira dubu dari biyu (₦200,000) ko kuma daurin sati biyu a gidan gyaran hali idan suka kasa biyan tarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here