Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano, ta yi gargaɗin samun matsala in ba’a biya kuɗin ajiya a kan lokaci ba

0
11
Hajji

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta roƙi masu niyyar zuwa aikin Hajji na shekara mai zuwa su gaggauta biyan kuɗin ajiyarsu domin sauƙaƙa shirin tafiya tun da wuri.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi, ya fitar, ya ce Darakta Janar na hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya yi wannan kira a yayin taron haɗin gwiwa da manyan limaman masallatan Juma’a da aka gudanar a dakin taro na Tourist Camp da ke Kano.

Alhaji Danbappa ya bayyana cewa buƙatar biyan kuɗin tun da wuri ta fito ne daga hukumar NAHCON da hukumomin Saudiyya, domin hakan zai ba su damar tsara jigilar alhazai, masauki da sauran shirye-shirye cikin lokaci.

Ya bayyana cewa kuɗin ajiyar kowane mahajjaci an amince da su ne a kan naira miliyan ₦8,244,813.67, inda ya shawarci masu niyyar zuwa aikin Hajji su hanzarta biyan kuɗin don guje wa matsaloli daga baya.

A nasa bangaren, wakilin NAHCON na yankin Kano, Alhaji Umar Muhammad Kalgo, ya yaba wa jihar Kano bisa jajircewarta wajen shirye-shiryen aikin Hajji, inda ya ce hakan na faruwa ne saboda tsare-tsaren gwamnati da wayar da kai da ake yi ga jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here