Dangote zai sayar da wani kaso na hannun jarin matatar sa

0
8
Aliko-Dangote
Aliko-Dangote

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce masana’antarsa ta tace man fetur na shirin sayar da tsakanin kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na hannun jarin ta a kasuwar hannayen jari ta Najeriya cikin shekara mai zuwa.

Ya bayyana cewa manufar hakan ita ce kada kamfanin ya riƙe fiye da kashi 70 cikin 100 na mallakar masana’antar.

 Dangote ya kuma ce suna shirin haɗa kai da kamfanoni daga ƙasashen Gabas ta Tsakiya domin faɗaɗa aikin tace mai da kuma gina sabuwar masana’anta a ƙasar Sin.

Haka kuma, masana’antar na shirin ƙara ƙarfin tace man daga gangar mai 650,000 zuwa miliyan 1.4 a rana, wanda zai sa ta zama mafi girma a duniya. Ya ƙara da cewa sun kusa kammala gyaran wasu na’urori a matatar, kuma za su dakatar da aiki na ɗan lokaci domin gyare-gyare kafin ƙarshen shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here