Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce tsarin zaɓe a Najeriya ya inganta sosai tun bayan da jam’iyyar PDP ta bar mulki a 2015.
Akpabio ya bayyana haka ne a zaman majalisar dattawa yayin karanta kudirin gyaran dokar zaɓe. Ya ce ya shafe kusan shekaru 25 cikin siyasa tare da Sanata Abaribe, kuma ya fahimci cewa yanzu zaɓe na tafiya da gaskiya fiye da baya.
A cewarsa, tun lokacin da tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua ya amince cewa zaɓen 2007 da ya kawo shi mulki cike yake da kura-kurai, an fara ɗaukar matakan gyara tsarin zaɓe a ƙasar nan.
Akpabio ya ƙara da cewa duk da ƙalubalen da ake fuskanta, tsarin zaɓe ya samu gagarumin ci gaba. “A baya, zabe yana cike da magudi, amma yanzu ana iya lashe zabe a ko’ina ba tare da takama da jam’iyya ba,” in ji shi.
Sanata Akpabio wanda yanzu yake jam’iyyar APC, ya taba zama gwamnan Akwa Ibom da Sanata a karkashin PDP, kafin daga bisani ya sauya sheƙa zuwa APC inda ya zama shugaban majalisar dattawa a 2023.


