Zazzaɓin Lassa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 172 a Najeriya–NCDC

0
11

Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasa (NCDC) ta bayyana cewa mutane 172 ne suka mutu sakamakon zazzaɓin Lassa a faɗin ƙasar nan tun farkon shekarar 2025 zuwa yanzu.

A cikin rahoton mako na 40 da hukumar ta fitar a ranar Talata, an tabbatar da samun mutane 924 da cutar ta kama a jihohi 21 da ƙananan hukumomi 106.

Wannan adadi ya fi na bara yawa, inda aka samu ƙaruwa daga kaso 17% zuwa 18.6% na mace-mace sakamakon zazzaɓin Lassa.

Rahoton ya nuna cewa jihohin Ondo, Bauchi, Edo, Taraba da Ebonyi ne suka fi fama da cutar, inda suka haɗa kimanin kaso 90% na dukkan alkaluman da aka tabbatar.

Ondo – 35%

Bauchi – 22%

Edo – 17%

Taraba – 13%

Ebonyi – 3%

NCDC ta ci gaba da gargadin jama’a su riƙa bin matakan kariya, kamar guje wa hulɗa da beraye, adana abinci da kyau, da kuma neman kulawar likita da wuri idan aka lura da alamun zazzabi mai tsanani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here