Sarkin Musulmi ya yi tsokaci a kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa zargin cewa ana kisan kiyashi da gangan kan Kiristoci a Najeriya ba gaskiya ba ne, yana mai cewa irin waɗannan ikirari ba su da hujja kuma manufarsu ita ce tada husuma tsakanin ‘yan ƙasa.
Ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin taron shekara-shekara na Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa da aka gudanar a Birnin Kebbi, jihar Kebbi. Sarkin ya ce babu wata shaida da ke nuna cewa ana aiwatar da kisan kiyashi a wani ɓangare na ƙasar, inda ya kalubalanci duk wanda ke da hujja ya fito da ita a fili.
Ya ƙara da cewa, Musulmi da Kiristoci sun dade suna zaune tare cikin zaman lafiya a Najeriya, kuma babu wata ƙungiya ta addini da aka yi niyyar kai wa hari na musamman. A cewarsa, matsalar tsaro ta shafi kowa, Musulmi da Kirista saboda duka suna fuskantar illolin ta’addanci, fashi da makami, da sauran laifuffuka masu nasaba da tashin hankali.