An kashe wata ma’aikaciyar jinya mai suna Hadiza Musa, wadda ke aiki a Asibitin Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan, Zaria, Jihar Kaduna, sakamakon harin da wasu masu ƙwacen waya suka kai mata yayin da suka yi ƙoƙarin kwace wayar ta.
Hadiza, wacce ita ce mataimakiyar shugabar sashen karɓar haihuwa a asibitin, ta rasu ne a ƙarshen makon da ya gabata lokacin da take kan hanyar ta ta komawa gida.
Mijinta, Hamza Ibrahim Idris, ya tabbatar da faruwar lamarin ga kafofin watsa labarai, inda ya bayyana cewa mutanen sun kai mata farmaki ne a kusa da gidansu kafin su tsere da wayar bayan sun jikkata ta.