Kotu ta bayyana matsayin ta a kan bayar da belin Tukur Mamu

0
9

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sake ƙin amincewa da buƙatar bayar da beli ga Tukur Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald, a shari’ar da ake yi da shi kan zargin tallafawa ta’addanci.

A hukuncin da alkalin kotun, Mai shari’a Mohammed Umar, ya yanke a ranar Laraba, ya ce kotun ta ƙi amincewa da roƙon belin Mamu duk da ikirarin cewa lafiyarsa tana fuskantar kulawa.

Sai dai kotun ta umurci Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) wadda ke tsare da shi, da ta kai Mamu asibiti mai inganci domin a duba lafiyarsa yadda ya kamata. Alkalin ya kuma ba shi damar zaɓar asibitin da yake so, tare da samun damar saduwa da iyalansa.

Mai shari’a Umar ya bayyana cewa lauyoyin gwamnati sun nuna jajircewa wajen gudanar da shari’ar, don haka babu hujjar bayar da beli bisa dalilin rashin ƙwazo daga ɓangaren masu ƙara.

Wannan dai shi ne karo na uku da kotu ke ƙin amincewa da belin Mamu tun bayan gurfanar da shi a ranar 21 ga Maris, 2023, bisa tuhumar aikata laifuka 10 da suka shafi tallafawa ta’addanci da sauran laifuka masu alaƙa da hakan.

An kama Mamu a ranar 7 ga Satumba, 2022, a filin jirgin sama na Cairo da ke Masar, inda daga baya aka dawo da shi Najeriya bisa zargin cewa yana da hannu wajen taimakawa ayyukan ta’addanci.

Gwamnatin tarayya ta zarge shi da shiga tsakani wajen tattaunawa tsakanin iyalan waɗanda aka sace a harin jirgin ƙasa na Abuja-Kaduna da ’yan Boko Haram, domin samun riba ta kashin kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here