Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta fitar da gargadi game da yiwuwar kai hare-haren ta’addanci da kungiyar ISWAP ke shirin kaiwa a wasu yankuna na jihohin Ondo da Kogi.
A wata takardar sirri da DSS ta aike zuwa ga kwamandan 32 Artillery Brigade na rundunar sojin Najeriya da ke Owena Cantonment, Akure, ranar 20 ga Oktoba, hukumar ta bayyana cewa ta samu bayanan sirri masu tabbatar da shirin ISWAP na kai hare-hare ga wasu al’umma.
Takardar, wadda Daraktan Tsaro na DSS reshen Ondo, Hi Kana, ya sanya wa hannu, ta bayyana garuruwan Eriti Akoko da Oyin Akoko a karamar hukumar Akoko North-West da kuma Owo a ƙaramar hukumar Owo a matsayin wuraren da ake kyautata zaton za a kai harin.
DSS ta ce an riga an fara leƙen asiri kan waɗanda ake zargin zasu kai harin a yankunan da abin ka’iya ya shafa, tana mai kira ga jami’an tsaro su ƙara kaimi don hana aukuwar wani mummunan lamari.
“Mun samu tabbataccen bayani cewa mambobin ISWAP suna shirin kai hare-hare a kan wasu al’ummomi na jihohin Ondo da Kogi nan ba da jimawa ba,” in ji rahoton DSS.