Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta fara a makon da ya gabata a dukkan jami’o’in gwamnati.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ya sanar da hakan a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a babban ofishin ASUU da ke Abuja a ranar Laraba.
A cewarsa, wannan mataki ya biyo bayan shiga tsakani da Majalisar Dattawa da wasu masu ruwa da tsaki suka yi domin kawo fahimtar juna tsakanin gwamnati da ƙungiyar.
Sai dai Farfesa Piwuna ya bayyana cewa, Majalisar Zartarwa ta ƙasa (NEC) ta ƙungiyar ta yanke shawarar bai wa gwamnati wa’adin wata guda domin ta magance dukkan matsalolin da suka jawo yajin aikin.