An saka lokacin bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Kamaru

0
12

An saka lokacin bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Kamaru

Majalisar Tsarin Mulki ta Kamaru ta bayyana cewa za ta sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar ranar 12 ga Oktoba ne a ranar Litinin mai zuwa.

A wata sanarwa da ta fitar a yau Laraba, majalisar ta ce ta kammala sauraron ƙorafe-ƙorafen da aka shigar mata kan zaɓen, inda ta yi watsi da mafi yawan buƙatun da suka nemi a soke wani ɓangare ko kuma gaba ɗayan sakamakon zaɓen.

An bayyana cewa za a fitar da sakamakon da misalin ƙarfe 11:00 na safiya agogon ƙasar a birnin Yaounde.

A makon da ya gabata, majalisar ta yi hasashen cewa za ta iya sanar da sakamakon a ranar Alhamis, kafin ta sauya wannan matsaya.

A halin yanzu, daruruwan jama’a sun fito kan tituna a manyan biranen ƙasar domin yin zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da abin da suka kira maguɗi a zaɓen.

Ɗan takarar adawa, Issa Tchiroma Bakary, ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen tare da kira ga Shugaba Paul Biya da ya amince da shan kaye, sai dai gwamnatin ƙasar ta yi watsi da wannan ikirari nasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here