An bayyana sunan mutanen da zasu shugabanci jam’iyyar PDP

0
6

Yayin da ake ƙara samun ɗumamar siyasa kafin babban taron jam’iyyar PDP na ƙasa da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba a garin Ibadan, Jihar Oyo, shugabannin jam’iyyar na yankin Arewa sun cimma matsaya kan mayar da kujerar shugabancin jam’iyyar na ƙasa zuwa yankin Arewa maso Yamma matakin da ake ganin zai taimaka wajen haɗa kan jam’iyyar kafin taron mai muhimmanci.

A cewar wasu manyan jagororin PDP da ke cikin kwamitin sauyin shugabanci, a taron da aka gudanar na shugabannin Arewa a Abuja a ƙarshen mako da ya gabata, an yanke shawarar cewa yankin Arewa maso Yamma ne zai samar da shugaban jam’iyya na ƙasa. Haka kuma, an amince cewa dukkan yankunan Arewa uku za su kammala tantance ‘yan takara a wannan makon.

Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa yankin Arewa maso Yamma na duba yiwuwar tsayar da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, tsohon Ministan Harkokin Musamman, Tanimu Turaki (SAN), da kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ahmed Makarfi. Sai dai rahotanni sun nuna cewa Tanimu Turaki na samun goyon baya tun daga farko daga yawancin shugabanni.

Wani babban jigo a jam’iyyar ya shaida wa jaridar The PUNCH cewa akwai yuwuwar Tanimu Turaki ya zama sabon shugaban jam’iyyar PDP, ganin yadda yake da goyon bayan muhimman shugabanni ciki har da gwamnonin jam’iyyar da suka rage.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here