Aƙalla mutane 73 aka sace bayan wani harin ‘yan bindiga a ƙauyukan Buzugu da Rayau da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.
Rahotanni daga Zagazola Makama, da ke bibiyar lamuran tsaro, sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:45 na safiyar Asabar, 18 ga Oktoba.
Shaidu sun ce ‘yan bindigar, waɗanda suka zo da yawa suna ɗauke da makamai masu ƙarfi, sun mamaye ƙauyukan biyu tare da yin awon gaba da mazauna yankin zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Majiyoyi sun ce ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an ceto mutanen da aka sace tare da dawo da zaman lafiya a yankin. Haka kuma, jami’an tsaro da ‘yan sa-kai na yankin sun haɗa kai wajen gudanar da bincike.