Shugaban ƙasa Tinubu ya naɗa Bernard Doro a matsayin sabon minista

0
4

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Dr. Bernard Mohammed Doro daga jihar Filato domin zama minista, inda nadin nasa ke jiran tantancewa da amincewar majalisar dattawa.

Bayo Onanuga, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabarun mulki, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Ya ce an riga an mika sunan Dr. Doro ga majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatarwa.

Dr. Doro ƙwararren masani ne mai gogewa fiye da shekaru 20 a fannoni daban-daban, ciki har da aikin likitanci, gudanar da harkokin magunguna, da shugabanci. Ya yi aiki a Najeriya da kuma Birtaniya, inda ya taka muhimmiyar rawa a tsarin kula da lafiyar jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here