Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa ta kama wasu jami’anta huɗu bisa zargin yin amfani da karfin iko fiye da kima yayin da suke tsare wani mutum a karamar hukumar Fufore.
Mai magana da yawun rundunar, Suleiman Yahaya Nguroje, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 14 ga Oktoba, 2025 a unguwar Sabon Gari, Fufore, inda aka ga jami’an suna amfani da karfi da kuma harbi a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Dankombo Morris, ya yi tir da halayyar jami’an, yana mai tabbatar da cewa za a dauki matakin ladabtarwa a kansu.
“Rundunar mu ba za ta lamunci rashin ladabi ko cin zarafi daga jami’anta ba. Doka za ta yi aikinta,” in ji Morris.
Ya roki jama’a da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare hakkokin jama’a tare da tabbatar da gaskiya da adalci a aikinta.