Mutane 30 sun rasu, 40 sun jikkata sakamakon fashewar tankar mai a Neja

0
6

Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 40 suka jikkata a wani mummunan hatsari da ya faru a kan titn Agaie-Baddegi da ke jihar Neja, bayan da tankar mai ta fashe.

Rahotanni sun nuna cewa, fashewar ta auku ne bayan da wasu mazauna yankin suka fara tattara man fetur da ya zube daga cikin tankar da ta yi hatsari. Sai dai kafin su ankara, tankin ya kama da wuta wanda ya lakume rayukan mutane da dama tare da lalata motoci da gidajen kusa da wurin.

Hukumomin tsaro da na kashe gobara sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce an kwashe gawarwakin wadanda suka mutu tare da kai wadanda suka jikkata asibiti don samun kulawa.

Wani mazaunin yankin ya ce, “Mun ji ƙarar fashewa mai ƙarfi, kafin mu ankara wuta ta bazu ko’ina. Wasu mutane suna ƙoƙarin ceto wanda wuta ta kama, amma wutar ta yi ƙarfi sosai.”

Gwamnatin jihar Neja ta bayyana alhini da tausayinta ga iyalan wadanda abin ya shafa, tare da yin kira ga jama’a da su guji ɗiban mai idan irin wannan hatsari ya faru don kauce wa sake faruwar irin wannan bala’i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here