Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Yi Wa Sojoji Karin Albashi

0
6

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar yin karin albashi ga jami’an tsaro, musamman sojoji, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro, domin rage musu radadin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar nan.

Shawarar ta zo ne kwanaki kadan bayan rahotannin da suka yadu na zargin yunkurin juyin mulki, rahotannin da fadar shugaban kasa ta musanta.

‘Yan majalisar sun ce jami’an tsaro na taka muhimmiyar rawa wajen kare Najeriya daga barazanar ta’addanci da rashin tsaro, don haka akwai bukatar gwamnati ta inganta rayuwarsu da albashinsu domin kara musu kwarin gwiwa a bakin aiki.

Sun kuma bukaci gwamnatin tarayya ta samar da ingantattun kayan aiki da tallafin jin kai ga iyalan jami’an da ke fuskantar barazana a yankunan da ke fama da rikici.

A halin da ake ciki, ana sa ran majalisar za ta tattauna da ma’aikatun tsaro da na kudi kan yadda za a aiwatar da shawarwarin cikin kasafin kudin shekara mai zuwa.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here