Kwankwaso yana da manufar samar da ci gaban Najeriya–Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin abokin samar da ci gaba, duk da cewa ya bar jam’iyyar APC.
A sakon taya murna da ya aika masa yayin da yake cika shekara 69, Tinubu ya ce Kwankwaso mutum ne mai akidar ci gaba da kishin kasa.
A cewar mai bawa shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, Tinubu ya taya iyalan Kwankwaso, abokansa da magoya bayansa murnar wannan rana ta musamman.
Ya yabawa Kwankwaso bisa gudunmawar da ya bayar a mukamai daban-daban da ya rike, ciki har da kasancewarsa tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Gwamnan Kano na wa’adanni biyu, Ministan Tsaro da kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya.
Tinubu ya ce tasirin siyasar Kwankwaso musamman a Arewacin Najeriya, na nuna irin siyasar jin kai da ya gada daga marigayi Malam Aminu Kano da Alhaji Abubakar Rimi.
“Kwankwaso aboki ne kuma abokin aiki tun lokacin Majalisar Kasa ta 1992, har zuwa lokacin da muka zama gwamnonin jihohinmu a 1999. Mun yi aiki tare wajen kafa jam’iyyar APC, duk da cewa daga baya ya koma NNPP, amma har yanzu yana cikin sahun masu akidar ci gaba,” in ji Tinubu.