Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bai wa wata matashiya mai suna Joy Ogah damar zama a kujerarsa na kwana ɗaya.
Lamarin ya faru ne a fadar shugaban ƙasa, lokacin da Shettima ya karɓi tawagar PLAN International karkashin jagorancin Helen Mfonobong Idiong.
A yayin taron, Shettima ya jaddada aniyar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen bunƙasa ilimin ’ya’ya mata a fadin ƙasar nan. Ya ce gwamnati za ta ci gaba da haɗin gwiwa da PLAN International domin tabbatar da aiwatar da shawarwarin da suka gabatar kan inganta ilimin mata.
Shettima ya kara da cewa ci gaban mata, musamman na yara mata, shi ne ginshiƙin cigaban ƙasa baki ɗaya.
A nata ɓangaren, Joy Ogah ta gode wa mataimakin shugaban ƙasa bisa wannan dama, inda ta ce mata na da ƙwarewar shugabanci idan aka basu dama da goyon bayan da ya dace.