EFCC ta ƙwato fiye da naira biliyan 500 cikin shekara biyu — Kashim Shettima

0
18

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta ƙwato dukiyar da ta haura naira biliyan 500 cikin shekara biyu da gwamnatin su ke mulki.

Shettima, ya faɗi hakan yayin da ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, a wajen taron bita na alƙalai da EFCC tare da haɗin gwiwar Hukumar Shari’a ta Ƙasa (NJC) a birnin Abuja.

Ya ce gwamnatin su ta ba wa ɓangaren shari’a da hukumomin yaki da cin hanci cikakken ’yanci domin gudanar da aikinsu ba tare da tsoma baki daga gwamnati ba.

“EFCC ta samu nasarar gurfanar da sama da mutum 7,000 a gaban kotu tare da ƙwato fiye da naira biliyan 500,” in ji shi.

Shettima ya ƙara da cewa kuɗaɗen da aka ƙwato ana amfani da su wajen shirye-shiryen tallafa wa jama’a, ciki har da shirin bayar da bashi ga ɗalibai da sauran manufofin jin daɗin al’umma.

Ya kuma yi kira ga alƙalai da ma’aikatan shari’a su ci gaba da gudanar da ayyukansu bisa gaskiya da adalci, yana mai gargadin cewa rashin bin adalci shi ke jawo matsaloli a ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here