Allah Ya kare ni daga masu neman raba ni da Kwankwaso–Abba

0
10

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi addu’ar neman kariya daga duk wanda yake kokarin haifar da sabani tsakaninsa da jagoransa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin cikar Sanata Kwankwaso shekaru 69 da haihuwa, wanda aka gudanar a gidan Kwankwaso da ke Miler Road, Kano, a yau Talata.

A cikin jawabin nasa, Gwamna Abba ya bayyana cewa duk wanda ke neman ganin an samu rabuwar kai tsakaninsa da Kwankwaso, “to sai dai ya tashi a banza, domin wannan dangantaka ta tabbata ne bisa girmamawa da kishin al’umma.”

Ya ce, “Allah ne ya ba mu jagoran da yake tsantsar kishin al’umma, wato Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Duk wanda yake kushe shi, to ba mai son ci gaban jama’a ba ne.”

Ya kara da cewa, “Munafukai na gida da na waje da ke kokarin raba ni da jagorana su sani cewa Kwankwaso, Abba, da mambobin jam’iyya muna nan tsayin daka waje ɗaya. Allah Ya kare mu daga masu neman tada fitina.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here