‘Yan sanda sun kama Lauyan Nnamdi Kanu

0
45

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta kama Lauyan shugaban ƙungiyar IPOB, Aloy Ejimakor, tare da wasu mutane yayin wata zanga-zanga da aka gudanar a Abuja.

Ejimakor ya tabbatar da kama su ne ta shafinsa na X inda ya bayyana cewa su na hannun sashin CID na Abuja.

A cewar sa, ‘yan sanda sun harba hayakin mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar da suka taru domin neman sakin Nnamdi Kanu, wanda ke tsare tun daga watan Yuni na shekarar 2021 a hannun hukumar DSS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here